Mutane 100 sun mutu inda 4000 suka jiggata ranadiyyar  wani abun fashewa  Lebanon

Ma’aikatan agaji a Lebanon ne kokarin dubo  daruruwan mutane da suka bace sakamakon fashewar abubuwan.

A kalla mutun 100 ne suka rigamu gidan gaskiya, yayin da mutane sama da 4000 suka samu raunika  a sanadiyyar fashewar wani abu  a Beirut babban birnin   kasar ta Lebanan.

Karfin fashewar ya girgiza daukacin birnin sannan ya lalata gidaje da gine-ginen da ke titunan da ke da nisan kilomitoci daga inda lamarin ya faru.

Shugaban kasar Michel Aoun ya ce ton fiye da 2,750 na wasu sinadirai na Ammonium nitrate da aka ajiye a wani wajen ajiye kayayyaki na tsawon shekaru shida ne ya janwo wannan barna.

Ammonium nitrate sinadirai ne da ake amfani da su wajen yin takin zamani domin noma sannan ana amfani da su wajen kera abubuwan fashewa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More