Mutane 5 ne suka rasu a Bahamas sakamakon Guguwar Dorian

Rahotunni sun nuna cewa Akalla mutum 5 ne suka mutu, yayin da muguwar goguwar nan ta Dorian ke ci gaba da lalata sassan tsibirin Bahamas.

Masu hasashen yanayi sun yi gargadin cewa goguwar ta Dorian ka iya ci gaba da tafka barna a tsibirin Bahamas nan da wasu awanni a gaba.

Firai ministan kasar Hubert Minnis ya ce an tabbatar da mace-macen mutanen ne a tsibirin Abaco, wanda barnar goguwar tafi yiwa tasiri kungiyar agaji ta Red Cross ta ce gidaje kimanin 13,000 akai tsammanin sun rushe zuwa war haka.

Shugaba Minnis ya ce, har yanzu wannan goguwa ta Dorian na da matukar hadari. Hotuna sun nuna yadda ruwan da ya yi ambaliya ke kara tudadowa, yana wancakali da motoci da watsi da itatuwa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More