Mutane 50 aka binne a kwana hudu cikin wata makabarta a Kano

Daya daga cikin masu kula da makabartar da ya nemi a boye sunansa ya ce tun daga ranar Juma’ar da ta gabata zuwa safiyar Litinin an binne kusan mutane 50 a makabartar Dan Dolo, wanda rabon su da su sami irin hakan tun lokacin da Boko Haram ta kai hari babban Masallacin Juma’a da ke Kano a shekarar 2011.

A makabartar Gidan Gona da aka fi sani da Makabartar Tarauni, wasu daga cikin masu kula da makabartar ya shaida wa BBC cewa tun kwanaki biyar da suka gabata yawan wadanda ake binnewa a makabartar ya karu.

Ya kara da cewa a safiyar Litinin kadai iya mutum hudu ne aka binne a makabarta, amma jumulla adadin wadan da aka kai makabartar sun kai kusan 55 sannan kusan mafi yawancin lokutan zafi da farkon kowane azumi sukan sami yawan gawarwakin da akan binne amma basu kai na wannan shekarar ba.

BBC ta rawaito cewa, Wakilin su  ya ziyarci Makabartar Dandolo da safiyar ranar Litinin ya ce ya hangi rukunin mutum uku da suka je makabartar daga unguwanni daban-daban domin kai gawarwaki don binnewa.

Farfesa Isa Sadik Abubakar, shugaban sashin cututtuka masu yaduwa na jami’ar Bayero da asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano ya ce, idan asibiti ba ya hayyacinsa ba ya bayar da taimako yadda aka saba, babu mamaki irin wadannan mutanen su shiga wani hali na shan wuya watakila ma a samu wasu daga cikinsu su rasu.

Ita ma gwamnatin jahar ta musanta cewa ana samun karuwar mace-mace.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More