Mutane 70 yan’ bindiga suka kashe a jahar Zamafara

Rahotanni daga jahar Zamfara na nuna  cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe fiye da mutane 70 a wasu hare-hare da suka kai wasu kauyuka a ranar Talata da kuma  Laraba.

Ganau sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun fara far wa mutanen kauyukan ne a ranar Talata inda suka kashe mutum 15, inda suka sake  far wa mutanen yayin da ake yin jana’izar wadanda aka kashe sa’annan ‘yan bindigar suka kashe mutum 50.

Abin ya faru ne a kauyukan Gidan Kane, Tungar Mawa, ‘Yar Gada da kuma wasu kauyuka da ke yankin.

Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da aka kai wa harin Kabiru Musa ya shaida wa BBC cewa mazauna kauyukan na cikin zaman ɗar-ɗar, sannan ya  cewa ‘yan bindigar sun zo Kauyukan kan babura fiye da 100, goyon uku-uku, yayin da suka kai harin
Ya bayyana cewa gawarwakin da ake yi wa jana’iza tun a farko dole aka bar su a yashe saboda babu yadda za a yi a ci gaba da jana’izar.  Kwamishinan tsaro na jahar Zamfara Abubakar Muhammad Dauran, ya tabbatar  wa da BBC cewa,  mutane 21 a aka kashe, inda  ya ce ana nan ana bincike kan asalin yawan mutanen da aka kashe.

Sannan ya kara da cewa akasarin barayin da suka kai harin sun gangaro ne daga jahar Katsina sakamakon fatattakarsu da ake yi kamar yadda suka samu rahoto.

Jahar Zamfara dai na daga cikin jahohin arewacin Najeriya da ‘yan bindiga suka addaba. A kwanakin baya, an samu saukin kai hare-haren, amma a halin yanzu abubuwan na neman ƙara sukurkucewa sakamakon yawan hare-haren ƴan bindiga.

A kwanakin bayan ne dai, sai da dakarun rundunar Hadarin Daji ta sojojin Najeriya suka kashe ‘yan bindiga da dama a jahar ta Zamfara.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More