Mutane 73 masu Cutar Coronavirus a Kano yanzu

Ma’aikatar lafiya ta jahar Kano ta tabbatar da karuwar mutane 14 da suka kamu da cutar Coronavirus, a daren Talata daga misalin karfe 11:58 wanda adadin ya kai 73

Jadawalin jahohin da cutar ta bulla da hukumar dakile cutuka masu yaduwa a Najeriya wato NCDC ta fitar ya nuna Kano ce ta uku a yawan masu fama da cutar bayan Legas mai mutum 430 da Abuja babban birnin kasar inda ake da mutane 118.

A ranar 11 ga watan Afrilu ne hukumomi a Kano suka sanar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar kuma tun daga wannan lokacin aka rika samun karuwar mutanen da annobar ta shafa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More