Mutum 3 sun mutu ta sanadiyyar wani jirgin helikwafta da yayi hatsari a jahar Legos

Wani jirgin helikwafta ya yi hatsari a garin Legas

Rahotanni sun ce akalla mutum biyu suka mutu a hatsarin da ya faru a Ikeja a yau Juma’a 28 ga watan Agusta 2020

Bayanai sun ce jirgin ya fadi a ginin wata coci ta sojoji a unguwar Opebi cikin Ikeja.

Bayan mutane biyu da suka mutu a hatsarin jirgin, mutum na uku da ke cikin jirgin wanda ya jigata, an garzaya dashi zuwa asibiti sashen kulawa da marasa lafiya na musamman sai dai shima ya rigamu gidan gaskiya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More