Mutum 34 yan bindiga suka kashe a Zamfara ranar Juma’a

Yan bindigar sun kai farmaki a kauyuka biyu, dake cikin karamar hukumar mulki ta Shinkafi, da yammacin Juma’a, tare da kaiwa mutanen da ke gonaki hari, sannan suka afkawa mutanen cikin garin.

An yi jana’izar sama da mutum 30 da suka rasa rayukansu sanadiyyar harin da ‘yan bindiga suka kai a yankin Shinkafi da ke jahar Zamfara.

Rundunar ‘yan sandan jahar Zamfara, ta tabbatar da aukuwar harin, inda ta ce tana daukar matakan dakile ayyukan ‘yan bindiga a jahar, kamar yadda SP Muhammad Shehu ya bayyana.

Harin ya biyo ne sa’o’i kalilan, bayan da sabon kwamishinan ‘yan sandan jahar ya fitar da sanarwarsa ta farko, inda ya sha alwashin ganin bayan mahara da masu satar mutane domin neman kudin fansa.

Amma ya ce zai ba da karfi wajen kokarin sasantawa da afuwa ga ‘yan bindigar da ke bukatar hakan.

Sai dai kuma jama’ar yankunan da ke fama da hare-haren na tababar tasirin wannan matakin, lura dacewa irin wannan yunkuri a can baya bai yi tasiri ba.

Tuni dai shi ma sabon gwamnan jihar Bello Muhammad Matawalle, ya kuduri aniyar fito da hanyar sulhu, domin dakile kalubalen tsaro a jahar, inda ya gudanar da tarurruka da Fulani, da ‘yan sa kai, da sarakunan gargajiya, da kuma jami’an tsaro.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More