Mutane 15 sun mutu sanadiyyar ambaliyar ruwa a jahar Sokoto

An tabbatar da mutuwar mutum 15 sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta faru a wasu kananan hukumomi shida a jahar Sokoto.

Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar wato NEMA ta ce sama da mutum 27,000 iftala’in ya shafa.

Kananan hukumomin da bala’in ya shafa sun hada da Goronyo, Rabah, Arewacin Sokoto, Wamakko, Silame, da kuma Binji.

BBC ta rawaito cewa, Rahoton da jaridar ta samu daga hukumar ya nuna cewa mutum 5,254 sun rasa muhallansu inda wasu mutum 12 kuma suka samu raunuka sakamakon rugujewar gine-gine.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More