Naira Miliyan 1,549,297 Kudin Aikin Hajjin maniyyatan Kaduna a 2019

Hukumar Jin dadin Alhazai ta jahar Kaduna ta sanar da kudin aikin hajjin bana a jiya Asabar 19 ga watan Mayu, inda ta ce dukkan maniyyaci zai biya naira 1.549,297,09 kamar yadda Hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta amince.

Mai sanya Ido akan ayyukan hukumar Sheikh Hussaini Suleiman Tsoho ne ya sanar da hakan a taron manema labarai da hukumar ta gudanar, inda yace, maniyyatan ana jiran su kammala biyan kudaden su kafin ranar 27 ga watan Mayun 2019.

A cewarsa, “A a yau muna sanar da kudin aikin hajjin bana a hukumace kamar yadda hukumar aikin hajji takasa NAHCON ta amincewa maniyyatan jahar Kaduna da su biya naira miliyan 1.549,549,09 da dako wanne maniyyaci zai biya kuma ko wanne maniyyaci zai biya kudin sa kafin ranar 27 ga watan Mayu na shekarar 2019 kafin mu kuma tuwawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON nan da ranar 30 ga watan Mayun shekarar 2019.

Sheikh Hussaini Suleiman Tsoho ya yi kira ga maniyyatan dasu gaggauta kammala biyan kudin nasu kafin zuwan lokacin da za’a rufe

A cewar Sheikh Hussaini Suleiman hukumar aikin hajjin ta kasa NAHCON ya zuwa yanzu ta warewa jahar Kaduna sama da kujeru 6,636 maniyyata tuni 3000 suka biya kudadaden su bayan da suka karbi takartun shaidar biyan kudin.
Inda a karshe ya kara da cewa, wayan da suke son su kara komawa aikin hajjin,na bana, zasu biya karin kudin saudiyya Riyals 2000 daidai da Naira 163,287.09.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More