Naira miliyan 46 Adamu Zango ya fiya kudin makarantar yara marasa karfi da marayu

Shahararren jarimin fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A. Zango ya biya wa wasu dalibai naira miliyan 46, kudin makaranta har na shekara uku.
Adamu Zango sanka takardar tabbatar da samun tallafin da ta fito daga makarantar Farfesa Ango Abdullahi da ke garin Zaria, a shafinsa na Instagram.
Takardar na nuna biyan kudin karatun yara 101 tun daga aji hudu zuwa kammala karatunsu na sakandare,wadanda yawancinsu marayu ne da kuma yaran da suka fito daga gidajen marasa karfi.
Amma jarumin bai yi bayani kan dalilan da yasa shi yin hakan ba, amma al’umma da dama sun sanya a shafukan su kama daga twitter, instagram da kuma facebook,wajen yi masa godiya tare da bayyana farin cikin su,yayin da wasu ke fatan yin koyi da abun alkairin da Zango ya aikata.

Saidai wannan bashi karo na farko da taurarin Kannywood ke tallafawa marasa karfi ba, amma fa wannan ne karon na farko da wani tauraro kannywood irin bajintar a lokaci daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More