Najeriya na iya samar da man fetur  ga nahiyar Afirka – Kyari

Sabon shugaban kamfanin man fetur na Najeriya ya ce kamfanin na shirin hada guiwa da wata sabuwar matatar man fetur mai zaman kanta da ake ginawa a jahar Lagos, domin mayar da kasar ta zamo mai samar da mai ga kasashen yankin.

Makasudin wannan yunkuri na hada guiwa da matatar man fetur din ta Dangote, wadda za ta rinka tace mai da ya kai ganga 650,000 a kowace rana, na daga cikin sabbin tsare-tsaren shugaban kamfanin Mele Kolo Kyari na yin garambawul ga kamfanin na NNPC ta yadda zai yi gogayya da takwarorinsa na duniya.

Matatar man fetur din da attajiri Aliko Dangote ke samarwa za ta zama wadda ta fi kowace girma a Afirka.

Kyari, wanda ke kokarin kara tabbatar da gaskiya a al’amuran kamfanin, ya shaida wa kamfanin dillancin labaru na Reuters cewa NNPC na so ya zama na farko da zai rinka samar wa matatar man ta Dangote da danyen mai.

Ya ce yarjejiniyar “wata kwantaragi ce ta samar da danyen man fetur.”

Kyari, ya ce zai wallafa sunayen wadanda ke gudanar da kwangilar danyen man fetur ta kasar, da kuma kamfanonin da suka yi nasara wurin samun aikin musayar danyen mai na Najeriya da tace shi,

Sannan kuma  zai bayyana rahoton asusun kamfanin wanda aka tantance.

Inda ya kara da cewa bayyana  ayyukan kamfanin da kuma shirin bunkasa harkar cinikayyar man fetur na kasar zai bunkasa zuba jari, wanda a baya ya gurgunce saboda rashin tabbas da rashin gaskiya.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More