Nasara na samuwa a Zamfara wajen gano wayanda akayi garkuwa da su.

Rundunar ‘yan sandan jahar ta Zamfara ta bakin kakakinta SP Muhammad Shehu ta shaida wa BBC cewa masu satar jama’a don karbar kudin fansa sun sako mutane da dama sakamakon zaman sasantawar.

Ya ce a bisa yarjejeniyar wadda Kwamishinan ‘yan sandan jahar Usman Nagoggo tare hadin guiwar gwamnatin jahar suka shirya, ‘yan kungiyar sa-kai sun saki Fulani 25 da suka kama.

Ya ce Kwamishinan ne da kansa ya je har garin Dansadau ya karbi mutanen sannan ya  damka su ga gwamnan jahar.

Bayan kwana daya  kuma aka  kuma karbo wasu mutanen guda 15, wadan Hausawa ne a garin na Shinkafi cewar  kakakin.

 

Haka kuma a wani daji da ke garin Gidan Dawa wanda ke karamar hukumar Kauran Namoda, da kuma wani a garin Kamarawa shi kuma a karamar hukumar Shinkafi, an karbo mutane 11, kamar yadda rundunar ‘yan sandan ta bayyana.

A bayanin da kakakin ya yi wa BBC ya ce dukkanin wadannan mutane 51 wadanda aka  yi garkuwa da su ne, ba a biya komai ba kuma  aka sako su.

Ya kara da cewa  a yanzu haka ‘yan sanda sun damka su gaba daya a hannun gwamnan jahar ta Zamfara, kuma nan ba da dadewa ba za a mika su ga ‘yan uwansu.

 

A bayanan da ya yi, ya kuma yace, nasarar ba ta tsaya a nan ba domin ana sa ran nan gaba ma za a sako wasu mutanen bisa wannan tattaunawa da hukumomin ke yi da ‘yan bindigar.

Sannan ya ce a yanzu an samu raguwar hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a jahar ta Zamfara a sakamkon tattaunawar da ake yi da su, wanda yana ganin idan tafiya ta kai tafiya matsalar tsaron da ke addabar jihar za ta zama sai tarihi.

Haka kuma wasu Fulani wadanda a da ba sa iya zuwa kasuwanni, a yanzu suna zuwa, domin ma yawanci kasuwanni a jihar sun bude, kamar yadda SP Shehun ya fada.

Jahar ta zamfara ta jima tana fama da matsalar tsaro lamarin da ya kai ga hallaka mutane da yawa da satar da dama domin karbar kudin fansa, lamarin da a baya-bayan nan ya fantsama wasu jihohin makwabtanta irin su Sokoto da Katsina.

Gwamnatin tarayyar Najeriyar ta sha bullo da matakan yaki da wannan matsala ta tsaro a jahar ta Zamfara, amma lamarin kusan ana ganin ya gagara duk da matakan tura sojoji da ake yi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More