Nasarar Buhari: Atiku ya ce da sake, ko wane mataki zai dauka?

Danoakttakarar shugaban Najeriya na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce bai amince da sakamakon zaben da aka yi wa Muhammadu Buhari ba.
Atiku ya ce abin kunya ne da zai kalubalanci zaben a kotu, amma haka ya zama wajibi domin ya ceto dimukaradiyyar Najeria ta ci gaba da dorewa.
Atiku ya ce a karni uku da ya yi yana siyasa, bai taba ganin yadda dimukaradiyyar Nageria ta ci baya kamar yadda aka gudanar da zabe a ranar Asabar ba.

Ya kara da cewar shi dan siyasa ne kuma akwai hanyoyi na siyasa da ya kamata a bayyana wa ‘yan kasa gaskiya domin duniya na kallon mu.
Atiku ya ce ta inda suka san an aikata abin da bai kamata ba shi ne yadda wasu jihohin da aka yi tashin hankali musammam wadan da aka tashi bama-bamai a lokacin zabe, sun samu kuri’u masu rinjaye.
Ya kara da cewar da akwai wasu jihohin da PDP ke da rinyaye an samu hatsaniya, inda mahukunta suka sa ido ba su magance rigin-gimu ba, kamar jihar Legas da Akwa Ibom da jihar Rivers.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More