NCDC ta aike da tawagar kwararru 17 Kano don taimakawa wajen yakar Covid19

Hukumar takaita yaduwar cutuka ta  Najeriya wato NCDC ta aike da wata tawagar kwararru 17 zuwa birnin Kano domin taimaka wa jahar yakar Coronavirus.

Bakwai daga cikin ‘yan tawagar sun fito daga Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO.

Babban jami’i a kwamiti na Musamman kan annobar Covid 19  na Najeriya, Dr Aliyu Isah ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da BBC.

Wannan dai na zuwa kwanaki biyu bayan da cibiyar da ke yin gwajin cutar  Coronavirus  a Kano ta ce ta rufe, sakamakon rashin kayan aiki.

Sai dai Dr Aliyu Isa ya ce sun aike wa da cibiyar kayan aiki, illa dai harbuwa da cutar Coronavirus  da jami’an masu yin gwajin suka yi ne da kuma yi wa dakin gwajin feshi ne dalilan da suka sa aka dage yin gwaje-gwajen.

Sakamakon dakatar da gwaje-gwajen a birnin na Kano, ya sa kwana biyu a jere hukumar NCDC da ma’aikatar lafiyar jahar ta Kano ba su fitar da alkaluman masu dauke da kwayar cutar ba.
Tuni dai gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nemi daukin gwamnatin tarayya, inda ya ce al’amarin ya fi karfi gwamnatin jaha tare da bukatar gwamnatin tarrayya tada tallafa wa gwamnatin tasa da naira biliyan 15 dan yakar cutar ta Covid19.

Gwamnatin Tarayyar dai ta bai wa jahar Legas tallafin kudi har naira bilyan 10.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More