NCDC tayi martani kan  watsi da gwamnatin Kogi tayi na bullar Coronavirus a jahar

Shugaban hukumar yaki da yaduwar  cutuka ta Najeriya wato NCDC, Chikwe Ihekweazu ya yi martani bayan gwamnatin jahar Kogi ta yi watsi da alkalluman da NCDC ta fitar da ke  nuna cewa,  an samu bullar cutar Covid19  a jahar,  wanda sakamakon ya nuna mutane biyu sun kamu da cutar,a jiya Laraba 28 ga watan Mayu 2020.

Kwamishinan Lafiya na jahar Kogi, Saka Haruna Audu, ya musanta hakkan, inda yace jahar tana da kayan gwaji, kuma ta gudanar da gwaje-gwaje musa yawan gaske, wanda babu wanda sakamakon gwajin da ya nuna akwai mai dauke da kwayar cutar ta Covid19.

Inda ya kara da cewa, matsin lamba  ba zai saka su amincewa da sakamakon duk wani gwaji da ba hukumar Lafiya ta jahar ce ta gudunar dashi ba.

Sai da kuma shugaban NCDC a birnin  Abuja ya yi watsi da ikirarin da gwamnatin Kogi ta yi,inda yace  babu wani kokwanto ko kuskure game da adireshin mutanen da aka yi wa gwaji daga jahar Kogi, kuma babu wata matsala dangane da  sakamakon mutum biyun da suka fitar sun kamu da cutar.

Munbi  bi kaidojin  Cibiyar Lafiya ta Tarayya, na tura su Asibitin Kasa,wanda  shine tsarin da ake bi idan mutum ya kamu.

Likitocin da ke asibitin sunyi zargin COVID19 ce bisa alamomin na majinyatan,  inda suka aika da samfurin  da yin gwaji, wanda sakamako  ya nuna suna dauke da kwayar cutar, ana laakari da inda mutum ya ke zaune ne wurin bibiyar harkar lafiya irin wannan,kuma an gano mutanen biyu mazauna Kogi ne.  Bayan sakamakon sun fito an sanar da babban likita mai sanka ido kan cututtuka masu yaduwa, wanda haka tsarin da yake. “Nauyi ya rataya a kan jahar ta gano wadanda suka yi cudanya da masu cutar kuma muna fatar za su yi hakan,” in ji shi.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More