NDDC: Majalisar dattawan Najeriya tace bata karbi miliyan 20 na tallafin Coronavirus ba

Majalisar Dattawan Najeriya ta bayyana cewar, babu wani mambanta da ya karbi kada sile daga Hukumar Raya Yankin Neja-Delta Wato Niger Delta Development Commission (NDDC).

Majalisar na mayar da martani ne ga shugaban bangaren ayyuka na kwamtiin riko a hukumar ta NDDC, Dr. Cairo Ojougboh wanda ya bayyana adadin kudin da ‘yan Majalisar Wakilai da ta Dattawa suka karba.

BBC ta rawaito cewa, Cairo Ojougboh ya fada wa wata jarida cewa hukumar ta bai wa kowanne sanata naira miliyan 20 sannan aka bai wa kowanne mamba a Majalisar Wakilai miliyan 15 a matsayin tallafin annobar Coronavirus.

Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar ya wallafa a yau Talata 1 ga watan Satamba 2020, ta musanta batun tana mai kalubalantarsa da ya wallafa sunayen sanatocin da aka bai wa kudin.

Sanata Dr Ajibola Basiru ya ce: “Majalisa ta karyata cewa babu wani sanata da ya karbi naira miliyan 20 ko wani kudi daga NDDC a matsayin tallafin Coronavirus  ko kuma wani dalili.

“Majalisa ta kalubalanci Dr Ojougboh ya kawo hujjar zargin da ya yi ta hanyar wallafa sunayen sanatocin.

“Idan ya gaza yin hakan, Majalisa na bukatar ya gaggauta janye maganar sannan ya nemi afuwar jama’a.”

A karshen makon da ya gabata hukumar karɓar korafe-korafe kan cin hanci da rashawa ta ICPC ta bayyana cewa ta fara bincike kan shugabannin NDDC bisa zargin almundahanar kudi naira biliyan biyar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More