Ngige bai cancanci ya dawo ma’aikatar kwadaga ba – Kungiyar kwadago

Kungiyar kwadago a Najeriya ta nuna rashin jin dadinta kan sake bai wa Chris Ngige ministan ma’aikatar ta kwadago a karo na biyu.

Tun bayan kawo karshen wa’adin mulkinsa na farko, Shugaba Buhari ya yi ikirarin cewa ministocinsa sun taka rawar gani, kuma shi ne dalilin da ya sa ya ci gaba da tafiya da wasu daga cikinsu.

Shugaban kungiyar kwadago a Najeriya kwamared Ayuba Wabba wanda ya yi korafin, ya shaidawa BBC cewa, “Ngige bai cancanta ya jagoranci ma’aikatar ba idan har gwamnati tana son yin aiki mai kyau da ma’aikata

Bayan sake rantsar da shi a matsayin ministan kwadago, Dakta Chris Ngige, ya yi alkawarin gaggauta aiwatar da sabon shirin mafi karancin albashi.

Wabba ya ce sun zata za a kawo wanda ya fahimci matsalolin ma’aikata, da sanin doka, idan har ana son a ci gaba da samun zaman lafiya da fahimta.

“Ba a sake dawo da wanda yake kamar soja ba, wanda kullum sai an yi ta daga wa  da shi,” in ji shi.

Ya kuma ce idan har gwamnati ta sake jan kafa kan wasu bukatunsu, za su ci gaba da daukar matakin da suka saba dauka.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More