Niba dalar Amurka bace da za’a sakani a aljuhu – Wike ga Ganduje

Gwamnan jahar Ribas Nyesom Wike, ya caccaki takwaransa na jahar Kano wato Dakta Abdullahi Umar Ganduje, bayan ya yi masa barazanar cewa zai maka shi kotu a kan rushe Masallaccin Jama’a a garin Fatakwal.

Gwamna Wike ya sha suka da tofin ‘Allah-tsine’ a kan zargin gwamnatin jihar Ribas da rushe babban masallacin garin Rainbow da ke yankin Trans-Amadi a birnin Fatakwal.

A wani jawabi da gwamna Ganduje ya fitar ranar Asabar, yayi ikirarin cewa zai maka gwamna Wike a kotu kan rushe masallacin.

Da gwamna Wike ke mayar da martani a kan kalaman Ganduje a cikin wani jawabi da mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Simeon Nwakaudu, ya fitar ya ce yayi Ganduje ya sani cewa shi ba takardar Dalar Amurka bane da za a iya saka wa a aljihun babbar riga a boye.

 

A cikin sanarwar, Gwamna Wike ya bayyana cewa ba zai taba gajiya wa da fadin cewa gwamnatinsa bata rushe kowanne Masallaci ba a jahar Ribas tare da bayyana cewa Jaridar Daily Trust da The Nation ne suka canja labarin domin cimma wasu manufofi na siyasa

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More