
Nicki Minaj zata gabatar da wasa a saudiyya menene ra’ayin ku?
An sanar da sunan Nicki Minaj a matsayin wadda za ta gabatar da wasa a dandalin wani taron raye-raye na shekara-shekara a Saudiyya, abin da ya jawo hayaniya a ciki da wajen kasar game da yadda abin zai kasance a kasa mai “tsauri” irin Saudiyya.
Mawakiyar hip pop din ta Amurka za ta gabatar da wasan ne a bikin Jeddah World Festival ranar 18 ga watan Yuli da muke ciki.
Wasan da za ta yi yana daya daga cikin irin sauye-sauyen da Saudiyya ke samarwa game da harkar nishadantsarwa a kokarinta na habaka bangaren adabi a kasar.
Sunan “Nicki Minaj” yana cikin kalmomin da suka yi fice a shafin Twitter a ranar Laraba yayin da mutane ke ta bayyana ra’ayoyinsu game da sanarwar.