NJC  ta bukaci Buhari  ya tabbatar  justis Tanko a matsayin Shugaban alkalan Najeriya

Shugaban kasar Najeriya  Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa da ta tabbatar da mukaddashin Shugaban alkalan Najeriya wato Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin tabbataccen Shugaban alkalan kasar.

Wasikar wanda Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisa a yau Alhamis, 11 ga watan Yuli 2019, shugaba Buhari yace bukatar ya biyo bayan shawarar da kungiyar alkalan Najeriya ta bayar na  cewar a tabbatar da mukaddashin CJN din.

Majalisar Alkalai Ta Najeriya (NJC) ta bukaci Shugaba Muhamamdu Buhari ya tabbatar da Alkalin Alkalai na wucin gadi, Justice Tanko Muhammad a matsayin tabbatacen Alkalin Alkalai na kasa.

An cimma wannan matsayar ne yayin wata taron gaggawa da majalisar ta gudanar karkashin jagorancin tsohon Shugaban Kotun Daukaka Kara na Kasa, Justice Umaru Abdullahi.

A cikin jawabin da Darektan Yada Labarai na NJC, Soji Oye ya fitar a ranar Laraba, 10 ga watan Yuli ya ce an cimma matsayar ne sakamakon rahoton da kwamitin da aka nada don tantance sabon alkalin alkalai na kasa ta gabatar da rahoton ta.

Tanko Muhammed ya kasance mukaddashin Shugaban alkalan kasar  Najeriya tun daga ranar 25 ga watan Janairu na shekarar 2019 bayan dakatar da tsohon Shugaban alkalan wato Walter Onnoghen.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More