Obasanjo ne babban mai raba kan ‘yan Najeriya – Buhari

Shugaban kasar  Najeriya Muhammadu Buhari yace  tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo na kokarin raba kan ‘yan Najeriya,  sakamakon irin kalaman da yake yi a ‘yan kwanakin nan.

Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ne ya fitar da sanarwar hakkan a ranar Lahadi, sanarwar ta bayyana cewa Shugaba Buhari yana kokarin hada kan ‘yan Najeriya ne da kuma gina kasar a ko ya yashe.

Obasanjon ya ce Najeriya na “lalacewa cikin sauri da kuma rabewa” karkashin a mulkin  shugaba Muhammadu Buhari.

Sai dai Shugaba Buhari ya ce Obasanjo ya zama babban mai raba kan yan kasa, kamar yadda sanarwar ta  Garba Shehu ta bayyana.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More