Ofishin kiran kar -ta kwana zai fara aiki da gaggawa a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bude ofishin karbar kiran kar-ta-kwana da wayar tarho a lokutan neman agajin gaggawa daga jami’an tsaro ko ma’aikatan kashe gobara ko asibiti ko kuma ma’aikatan kiyaye haddura.
Ministan sadarwar kasar Najeriya Dakta Isa Ali Pantami ne ya shaida wa BBC hakan, inda ya ce tuni gwamnatin ta bude ofishin farko na wannan tsarin a jahar Katsina matakin da ya bai wa sama da mutum 40 aikin yi.

A cewarsa, an yi tanadi ga masu neman agajin gaggawa su kira lambobin 1-1-2 a duk lokacin da suke da bukatar dauki a kan tsaro da al’ummar kasar ke kokawa akai.
Ya ce ko da mutum ba shi da kudi a wayarsa, yana iya kiran wannan lamba kuma nan ta ke za a hada shi ga ofishin cikin sauki.

Dakta Pantami ya kara da cewa wannan tsarin, da ba sabon abu ba ne a duniya, zai fara aiki a fadin jahohin kasar 36 har da babban birnin tarayya Abuja nan ba da dadewa ba.
Ministan ya ba da misali da kasar Amurka inda take da wannan tsarin na kiran lambar 9-1-1, wanda suka shafe kusan shekara 50 su na yi.

Ya ce a duk shekara, wannan lamba ta 9-1-1 ana kiran ta domin neman agajin gaggawa sau miliyan dari biyu da arba’in, kashi 75 na adadin ‘yan kasar Amurka kenan.
Game da karin alfanun wannan yunkuri kuwa, Pantami cewa ya yi matakin zai bude kofar samar wa matasa ayyukan yi.
Ya ce kasa da kwana 30 da zama ministan sadarwa ne ya kaddamar da wannan cibiya da gwamnatin baya ta samar cikin shekarar 2005, kusan shekara 14 kenan da samar da cibiyar.

Akwai manufata a yin, ba wayonka ko iyawarka ba, Allah ya sa an fara yin nasara. Ina ganin cewa Allah zai duba kyakkyawar manufarmu da fatan alheri da addu’oin da ‘yan Najeriya suke yi a gare mu, a cikin takaitaccen lokaci wajen cigaba da kaddamar da cibiyoyin a kuma tabbatar suna aiki” kamar yadda Pantamin ya bayyana.

Ministan ya ce yana fatan wannan ci gaba ya karade wurare da dama a Najeriya cikin shekarar nan.
Dakta Pantami ya kara da cewa wannan sabon tsarin ba zai ci karo da tsarin da wasu hukumomin tsaro suke da shi na lambobin kira don kai daukin gaggawa ba, yana mai cewa wannan tsarin karkashin hukumar kula da kamfanonin sadarwa ta kasar, zai kasance mafi sauki kuma mai inganci akan makamantan irin sa da ake da su.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More