Oshiomhole ya daukaka kara kan hukuncin dakatar dashi da kotu tayi

 Adams Oshiomhole ya daukaka kara a kan hukuncin wata babbar dake kotu  tayi na dakatar da shi daga matsayin sa na shugaban jam’iyyar APC ta kasa, ta hanyar umarta sa , da ya koma gefe har zuwa lokacin da aka yanke hukunci kan karar da aka shigar a kansa a kotu na neman tsige shi baki daya daga mukamin nasa.

 

A takardun da ya gabatar na daukaka karar, Mista Oshiomhole ya soki hukuncin da kotun ta yanke.

 

 

 Wadanda ya yi karar sun hada da mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa (yankin Arewa maso Gabas) Mista Mustapha Salihu, da kuma shugaban jam’iyyar reshen jahar Edo, Anslem Ojezua wanda ke biyaya ga gwamnan jahar Mista Obaseki

 

 Legit ta rawaito cewa, sauran sun hada Sani Gomna, Oshawo Steven, Fani Wabulari, Princewill Ejogbarado, Sufeta Janar na ‘yan sandan Najeriya da kuma Hukumar ‘yan sandan farar hula SSS.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More