Osinbajo ya ziyarci jahar Kano dan bude manyan ayyuka

Mataimakin Shugaban Najeriya ferfesa  Yemi Osinbajo, ya  ziyarci jahar Kano dan kaddamar da wasu manyan ayyuka wanda gwamnatin Dakata Abdullahi Umar Gandujue ne ya gudanar da ayyukan.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje,mataimakinsa Nasiru Gawuna  tare da wasu manyan jami’an gwamnati ne  suka tarbi Osinbajo a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano,

Ferfesa Osinbajo  zai kaddamar da gadar Alhassan Dantata da ke unguwar Sabon Gari da gadar Tijjani Hashim da ke unguwar Kofar Ruwa duk a cikin jahar ta Kano,zai kuma kafa tubalin wasu ayyuka da gwamnatin jahar za ta fara gudanar wa.

A lokacin ziyarar aikin na kwana daya a jihar, mataimakin Shugaban kasar zai assasa tushen gini na cibiyar kansa mallakar jaha ta farko a Najeriya.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More