PDP ta kori tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Jigawa

Jam’iyyar PDP ta kori tsohon dan takarar ta na gwamnan Jigawa, Aminu Ibrahim,saboda yin zagon kasa ga jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Alhaji Ibrahim Babandi, shine ya fadi hakan yayin ganawa da manema labarai a garin Dutse ranar Laraba.
Babandi ya ce an kori Ibrahim din ne bayan ya gaza bayyana tare da kare kansa a gaban kwamitin da aka kafa don binciken zargin da ake yi masa.
“Membobin ‘yan jaridu, mun gayyace ku don sanar da ku shawarar da Kwamitin Zartarwa na PDP ya yanke game da
wasikar da muka karba daga mazabar Ibrahim a Ringim.
“Kimanin makonni uku da suka gabata, mun samu wasika daga Ringim cewa an dakatar da tsohon dan takararmu na gwamna, Malam Aminu Ibrahim Ringim saboda yin ayyukan adawa ga jam’iyya da zagon kasa da yake yi.
“Sun yanke shawarar dakatar da shi na tsawon wata daya sannan suka aiko mana da wasika a matsayin Kwamitin Zartaswar Jiha na jam’iyyar, wanda muka duba da kyau. “Bayan mun duba wasikar, mun duba kundin tsarin mulkin jam’iyyar wanda ya tanadi cewa ya kamata mu kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin, kuma mun yi hakan,” in ji shi.
Babandi ya kara da cewa, “Kwamitin ya yanke shawarar gayyatar duka kwamitin gudanarwa na mazabar da kuma wanda ake bincika.
“Bayan gayyatar, kwamitin, karkashin jagorancin Alhaji Muhammad Daguro, ya tabbatar a cikin rahotonsa cewa an gano Ibrahim ne ya aikata ayyukan. ”
Ya ce kwamitin ta gayyace shi har sau biyu ya bayyana don ya kare kansa a gaban kwamitin, amma ya kasa yin hakan.
“Mun rubuta masa wasika amma ya yanke shawarar ba zai bayyana a gaban kwamitin ba har sau biyu a jere, kuma an shawarce mu da mu dauki mataki na gaba, wanda shi ne korarsa daga jam’iyya, kwatankwacin shawarar kwamitin, wanda muka amince da shi, ”In ji shi.
A cewarsa, kwamitin zartarwa na jam’iyyar ya bukace shi da ya daina nuna shi a matsayin dan jam’iyyar daga yanzu.
Lokacin da aka tuntube shi, Ibrahim ya ce Kwamitin Zartarwar Jihar ba shi da ikon fitar da shi daga jam’iyyar.
Ya ce an kirkiro shugabannin gudanarwar ba bisa ka’ida ba saboda haka ba su da ikon gayyata ko daukar mataki kan kowane dan jam’iyyar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More