Ramadan: Gwamnan Zulum ya bukaci al’umma dasu yi addu’a kan Boko Haram da Coronavirus

Gwamnan jahar Borno Babagana Zulum ya roki al’ummar Musulmin jahar da ka da su manta wajen gabatar da addu’o’i kan Allah ya karya kungiyar Boko Haram da magoya bayanta.

Zulum ya bayyana hakan ne a wata sanarwar da mai tamakamasa a bagaren yada labarai Isa Gusau ya fitar.

Ya bayyana cewa, a kwana 10 na karshen watan Ramadan mai alfarma, akwai yiwuwar musulman duniya za su mayar da hankalinsu ne kan yin addu’a a kan Coronavirus, ko shakka babu cutar annoba ce mai yi wa bil adama barazana. Ina rokon Musulman Najeriya ka da su manta da irin barnar da Boko Haram ke yi. Inji Gwamnatin Zulum
Muna da annoba guda biyu a yanzu, wadanda matsayinsu da barazanarsu iri daya ce.

Hakkan ya biyo baya ne bayan da gwamnatin jahar ta Borno ta sake bude masallatai da majami’u a sakamakon gamsuwar da ta ce ta yi da yadda mazauna jahar ke bin dokokin kare kai daga kamuwa da cutar ta Covid19.

Mataimakin gwamnan jahar Borno, kuma shugaban kwamitin yaki da Covid-19 a jahar,Umar Usman Kadafur, ne ya fitar da sanarwar, inda ya ce za a iya ci gaba da gudanar da ibadu a masallatai da majami’u amma da sharadin bayar da tazara da juna da kuma saka takunkumin rufe fuska.

Sai dai sanarwar gwamnatin ta bayyana cewa ba za a gudanar da Sallar Idi ba saboda ba farilla ba ce, hakan na nufin ranar sallah mabiya addinin musulunci za su zauna a gidajen su.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More