Rana irin ta 12 ga wata Junairu

Ko kun san a rana ta 12 ga wata tsagerun yan tawayen Biafra suka saduda suka mika wuya?

• A 30 ga Mayu, 1967 tsagerun yan tawayen Biafra suka ayyana ballewa daga kasar Najeriya tare da kafa cantacciyar kasar Biafra.

Sai dai kuma bayan shafe shekaru biyu da rabi ana yakin Basasa, a rana mai kama ta yau 12 ga Janairu,1970 tsagerun dakarun yan tawayen name Biafra suka saduda, suka mika wuya bayan ratattakarsu da dakarun sojin Najeriya suka yi.

Yunkurin ballewar da yan tawayen suka yi ya haifar da rasa rayukan yan Biafra kimanin mutum miliyan biyu.

• Haka zalika a rana mai kama ta yau a 2006 aka sami sami rasa rayukan mahajjata kimanin 362 a wajen jifan shaidan a Mina.

• A rana dai mai kama ta yau amma a 1915 majalisar wakilan kasar Amurka ta yi watsi da kudirin dokar da zai bawa mata damar yin zabe a jihohi.

• sai dai kuma shekaru 17 bayan majalisar ta kasar Amurkan ta hana matan na Amurka samun dakar kada kuri’a, a shekarar 1932 Hattie Caraway ta zama mace ta farko da aka zaba a matsain yar majalisar dattawan kasar ta Amurka.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More