Ranar Dimokuradiyya : Gwamnatin Najeriya ta ayyana Juma’a a matsayin ranar hutu

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranar Juma’a 12 ga watan Yuni a matsayin hutu na Ranar Dimokuradiyya ga ma’aikata.

Sanarwar da Sakatariya a ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar, Georgina Ehuriah a madadin Minista Ogbeni Rauf Aregbesola, ta ce ministan ya taya ‘yan Najeriya murnar ɗorewar mulkin dimokuraɗiyya.

Wannan ne karo na uku da za a yi bikin Ranar Dimokuraɗiyya ranar 12 ga watan Yuni tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sauya ranar daga 29 ga watan Mayu a ranar 6 ga watan Yunin 2018.

Ministan harkokin cikin gida ya shawarci ‘yan Najeriya da su ci gaba da bin umarnin masana harkar lafiya domin kare kansu daga annobar Coronavirus wadda zuwa yanzu ta yi ajalin mutane 361 sannan ta kama mutane 12,80, Inda aka sallami mutane 4,040 a kasar ta Najeriya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More