Ranar June 12 : Yau ne ake  bikin zagayowar Dimokradiyya a Najeriya

Wannan rana ta 12 ga watan Yuni, ta kara karfi ne bayan da gwamnatin mulkin dimokradiyya ta zauna da kafarta a 1999.
An rinka gudanar da bikin wannan rana ne tun daga shekarar 2002, haka kuma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karawa wannan rana karfi a shekarar 2018 bayan da ya sauya ranar dimokradiyya daga ranar 29 ga watan Mayu zuwa ranar 12 ga watan Yuni.

Sauya ranar Dimokradiyya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni bai yi wa wasu ‘yan Najeriyar dadi ba inda har wasu na ganin cewa siyace kawai.

Wannan rana da galibin al’ummar Najeriyar suka fi sani da June 12, rana ce da tarihin kasar ba zai manta da ita ba saboda a ranar ce aka gudanar da zaben Najeriya na 1993, kodayake har kawo yanzu hukumar zaben Najeriyar bata sanar da wanda ya lashe zabenba.

To sai dai kuma dukkan alamu sun nuna cewa dan takarar jam’iyyar SDP, wato Moshood Kashimawo Olawale Abiola, ne ya lashe zaben inda ya kayar da abokin takararsa na jam’iyyar NRC Bashir Othman Tofa.

An dai ki sanar da sakamakon zaben ne saboda soke zaben da gwamnatin mulkin soja a karkashin mulkin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta yi.

Wanda soke zaben  ya janyo gagarumar tirjiya daga ‘yan jam’iyyar SDP da kuma ‘yan gwagwarmaya da ke da rajin kafa gwamnatin farar hula a wancan lokaci abin da ya kai ga tsare wasunsu da dama ciki har da Abiola.
Shekarun baya, an saba gudanar da bikin ranar dimokuradiya a ranar 29 ga watan Mayu na kowace shekara kafin shugaba Muhammadu ya sauya ranar a shekarar 2018.
Buhari ya yi hakan ne domin karrama marigayi Moshood Abiola da babbar lambar yabon kasar ta GCFR, da kuma  tunawa da zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993.

A kowacce rana irin wannan gwamnatin Najeriyar kan bayar da hutu ga ‘yan kasa, sannan ta shirya biki a matakin tarayya, haka suma jahohi kasar musamman na shiyyar arewa maso yammaci kan shirya irin wannan biki da nufin tunawa da ranar da aka yi zaben 12 ga watan Yuni.
A wannan karon dai za ayi bikin zagayowar wannan rana cikin yanayi na annobar cutar Coronavirus  abin da ake ganin bikin wannan shekarar ba zai yi armashi ba saboda yanayin da ake ciki.

A Najeriya, ranar 12 ga watan Yunin kowacce shekara ita ce ranar bikin zagayowar Dimokradiyya ta kasar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More