Rashin dawowar Buhari Najeriya yasa aka soke kaddamar da ayyuka a Imo

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya soke ziyarar aiki da zai kai jahar Imo domin kaddamar da wadansu ayyuka.

An sa ran shugaba Buhari  zai isa jahar Imo a yau 21 ga watan Mayu dan  kaddamar wasu ayyukan da gwamnatin jahar ta yi tare da kaddamar da mutum-mutumin shugaban kasar da aka gina a Jahar.

Tawagar ‘yan jarida sun isa birnin Owerri domin daukar rahoton ziyarar da shugaban kasar zai kai.

Daga bisani  Sakataren watsa labaran gwamnan  Imo, Sam Onwuemeodo ya tabbatar da cewa: shugaban Buhari ya soke zuwansa jahar  Imo sakamakon rashin dawowar sa  daga kasar Saudiyya da je dan gabatar da umarah.

Hakan ya saka aka fasa kadammar da ayyukan  a yau 21 ga watan Mayu 2019, tare da shirin saka wata ranar.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More