Rashin gaskiya na karuwa a Najeriya idan a kwata da kasashen Afrika – Attahiru Jega

Menene ra’ayin ku game da hakkan?

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta wato INEC Farfesa Attahiru Jega, ya shawarci kasashen Afrika su sauya salon yakin da su ke yi da rashin gaskiya a halin yanzu.

Farfesa Attahiru Jega ya rike hukumar zabe mai zaman kan-ta a Najeriya tsakanin 2010 zuwa 2015.
Jega ya bayyana hakkan ne a lokacin da ya ke yin tanbihi a kan wani sabon littafi da hukumar EFCC ta kaddamar mai suna “Curbing Electoral Spending” (magance kashe-kashen kudi a lokacin zabe), inda yake nuna cewa akwai matsala a kasar ta Najeriya.

An shirya kaddamar da littafi ne a ranar bikin yaki da rashin gaskiya ta Duniya a ranar Litinin 9 ga Watan Disamba 2019.

Jega ya kara da cewa, rashin gaskiya na karuwa a Najeriya, idan aka kwatanta da sauran kasashen Afrika, kuma ya kamata muyi duba a kai domin yin yakin da gaske wajen yin duba bisa tafiyar da ake ciki a yanzu haka, dan rana ce da zamu yi karatun ta natsu dan gano dabarun yin yaki da rashin gaskiya.

A karshe Jega ya yabawa kokarin da EFCC ta ke yi wajen yakar satar dukiyar gwamnati da rashin gaskiya, tare da bukatar zage dantse wajen ganin babu sanayyar a wajen gudanar da ayyukan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More