Rasuwar marigayi Sarkin Zazzau: Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana zaman makoki na kwana uku

Rasuwar marigayi Sarkin Zazzau: Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana zaman makoki na kwana uku

Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana zaman makoki na kwana uku domin alhinin rasuwar sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rigamu gidan gaskiya a ranar Lahadi 20 ga watan satamba.

Mai bawa gwamna El-rufa’i shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Mista Muyiwa Adekeye ne ya sanar da hakan yau  Litinin.

Adekeye ya ce za a bude ofisoshin gwamnati a ranakun 21 da 22 na Satumba, amma banda a ranar 23 ga don yin addu’a ga marigayi sarkin, sannan kuma  za a saki tutoci kasa-kasa domin alhinin rashin nasa.

Sarki ya rasu a asibitin Sojoji na 44, dake jahae Kaduna,  yana da shekara 84.

Babban limamin masarautar Zazzau, Dalhatu Kasimu ne ya jagoranci sallar jana’izarsa da aka gudanar a fadarsa dake Zari’a, da misalin karfe 5:35 na yamma, wanda dubban mutane suka halarta.

Daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada gwamna Nasiru  El-Rufai, Sakataren Gwamnatin jihar  Kaduna Balarabe Lawal-Abbas, Kakakin majalisar jihar ta Kaduna Yusuf Zailani, da sauran manyan jami’an gwamnati.

Har ila yau, a fadar akwai mai martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, shugabannin sojoji, da masu samar da kayan agaji ta jihar Kaduna.

An nada Alhaji Shehu Idris a matsayin Sarkin Zazzau a ranar 15 ga Fabrairu shekarar 1975, marigayi sarkin, shine sarkin Zazzau na 18, kuma ya kasance shugaban majalisar sarakunan jihar Kaduna, inda ya yi sarauta na tsawon shekaru 45, kafin rasuwarsa.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More