Real Madrid ta sha kashi a gida a hannun Barcelona

Real Madrid ta sha kashi har gida a hannun Barcelona da ci 3-0 a wasan gab da na karshe na gasar Copa del Rey.

Luis Suarez ne ya fara bude wa Blaugrans din asusun jefa kwallo a raga a minta na 50 bayan da ya d’ad’a kwallo a raga da bugun kurosin din da Dembele ya yi masa. Raphael Varane ya rubanya nasarar ta Barcelona da kwallon da ya ci gida a minti na 69.Luis Suarez ya sake jefa kwallo a ragar Madrid a minti na 73 da bugun fenareti bayan da Casemero yayi masa keta.

Za a buga wasan karshe na gasar ta Copa del Rey a 25 ga Mayu inda Barcelona zata kara da ko dai Real Betis ko Valencia

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More