Rikici ya barke a jam’iyyar PDP ta Kano

Rikici ya barke a jam’iyyar PDP ta Kano

Shugabannin da ke rike da jam’iyyar adawar a kananan hukumomi 44 na jahar Kano ne su ka sanar da ‘Yan jarida wannan a Ranar Laraba.
Daily Trust ta rawaito cewa, Mahammina Bako Lamido aka nada a matsayin shugaban rikon kwarya na PDP

Mahammina Bako Lamido ya dare kan kujerar ne kamar yadda ya bayyana a Sakateriyar jam’iyyar bayan an tsige majalisar Injiniya Rabiu Bichi.

Dokar PDP ce ta bada damar a sauke shugabannin rikon kwaryar da ke kan kujerar a baya, cewar sabon shugaban jam’iyyar da aka kafa.

Bako Lamido ya ce sashe na 31 (2) (e) na kundin tsarin mulkin PDP ya ba shugabannin rikon kwarya wa’adin watanni uku ne rak.

Bako Lamido ya ce sun sanar da hedikwatar jam’iyya PDP da ke babban birnin tarayyar Abuja game da cikar wa’adin shugabannin da ke rike da jam’iyyar tun 2019.

Duk da cewa shugabannin kananan hukumomi sun aikawa uwar jam’iyya takarda a 2019, ba a dauki matakin kauda su daga mukamansu ba. Wannan ya sa wadannan jagorori na jam’iyyar hamayyar su ka ruguza shugabannin da aka kafa bayan dawowar Dakta  Rabiu Musa Kwankwaso jam’iyyar ta PDP.

Saida Rabiu Bichi ya ce har yanzu shi ne Shugaban PDP a jahar ta Kano Source: Twitter

Oaktv ta kira shugaban kungiyar gangamin matasa ta jam’iyyar PDP Ibrahim Bala Aboki, ta wayar tarho inda ya shaida mana cewa suna sa ran taron gudanar zabekan jaddada shugabanci na mazabu, jaha da kuma na jam’iyyar, wanda za’a gudanar da taron a Eangle square dake babban birnin tarayyar Abuja.

A yanzu haka an fara saida fim din, da zai bada damar a gudanar da duk wani sauye-sauyen daga wannan wata da muke ciki har zuwa wantan Afirlu 2020, inji Bala.

Sannan ya kara da cewa a yanzu dai su a jahar Kano Rabi’u Suleiman Bichi suka sani har yanzu a matsayin shugaban jam’iyyar PDP na jahar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More