Rikicin APC: Gaidom ya bayyana kansa a matsayin sabon Shugaban riko na APC

An shiga rudu a jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya bayan da mataimakin babban sakataren jam’iyyar na kasa, Victor Giadom ya bayyana kansa matsayin sabon shugaban jam’iyyar na riko.

Sabon shugaban riko na jam’iyyar ta APC Victor Giadom, ya soke zaben fidda gwani na gwamnan jahar Edo a Najeriya.

Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa,Mista Giadom yace ya dauki matakin ne bisa umarnin da kotu ta bayar a baya wanda ya ba shi damar yin hakan.

Sannan kuma yace, ya samu goyon baya Daga mambobin Kwamitin Gudanarwa na Jam’iyyar ta APC.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More