Rikicin APC: Nan da kwanaki kadan zamu dauki matakin shawo kan rikicin – Ahmed Lawan

Menene ra’ayinku game hakkan?

Shugaban majalisar dattawan Najeriya Ahmad Lawan ya ce za a shawo kan rikicin jam’iyyar ne kawai idan aka yi biyayya ga tanade-tanaden kundin tarin mulkin nata.

Ahmed ya  bayyana haka ne bayan ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja ranar Lahadi.

Ya kuma bayyana cewa, yayi amanar dole sai sun bi kundin tsarin mulkin jam’iyyarsu ta APC  sannan su lura da  yada za su magance  masalolin,  sannan  a yayin yin dubun, ya zama dole a hana rikicin ya ci gaba da faruwa kamar yadda ya wallafa a shafisa na Twitter. “Ina so na tabbatarwa dukkan mambobin jam’iyyarmu  ta APC cewa da yardar Allah, nan da kwanaki kadan, za mu ga yadda za a dauki matakin shawo kan rikicin”.inji shugaban majalisar dattawan Najeriya

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More