Rikicin Ganduje da Sanusi ya kamata a shiga al’amarin – Sheikh Dahiru Bauchi

Babban malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi yayi kira ga dukkanin masu ruwa da tsaki da su sanya baki a na  lamarin rashin jituwan da ke tsakanin Sarkin Kano, Mohammad Sanusi II da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Ya bayyana hakan ne  wata hira da manema labarai a gidansa da ke Bauchia a jiya Lahadi 30 ga watan Yuni 2019, inda yake cewa, garin Kano ta kasance jaha mai mahimmace a Najeriya  dan hakan abun da ya faru a Kano tsakanin masarautar jahar da gwamnatin jahar ba bun jin dadi bane, abun bakin ciki ne.

Yace ya kamata  Gwamnan ya ba masarautar girmanta kuma dole masarautar ma ya ba da girma ga gwamnati. Dole a girmama masarautan saboda tana bayar da umurnin ga mutane kuma siyasa ba zai yiwu ba idan ba tare da goyon bayan mutane ba yayin da, a bangarenta, dole masarautar ta fahimci cewa lokuta sun canja, gwamnatin na da alhakin nada sarakuna.

 

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More