Rikicin Zamfara yafi na Binuwai Da Taraba tsamari – Buhari

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, kashe kashen da ake yi a jahar Zamfara ya fi kashe kashen da ake yi a yankin jahohin Binuwai da Taraba, duba da yanda aka fi samun labaran tashin hankali a yan shekarun nan.

 Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise TV,bayan yi masa  tambaya  dalilin karuwar rikice rikice a jahohin Katsina, Binuwai,Filato, Zamfara da kuma Jahar Borno, shugaban kasa Muhamadu Buhari  ya bayyana cewa, “Matsalar ita ce, gidajen watsa labarai na iya taimaka wa wajen samar da zaman lafiya wurin yada labaru masu kwantar da hankali da kuma kira ga gudanar da shugabanci na gari.

Inda yace babar matsalar a halin yanzu ita  kashe kashen da ake yi a yankin jahohin Taraba, Binuwai basu kai mutanen da ake kashewa a jahar ta Zamfara ba amma abin takaicin shi ne shugabanin wadannan jahohin na bayar da bayanan dake nuna cewa kamar  ana rikici ne bisa kabilanci da addini kuma wannan bai dace ba ga al’ummar Najeriya.

Shugaban kasar ya kara da cewa, a bayyana ne yake cewa, makiyaya na daukar sanda a duk inda suke tafiya don kiwon shanayansu da kuma adduna wanda suke amfani da shi wajen karyo itace da ciyawa don ciyar da dabbobinsu.

Ya kuma kara da cewa, bayan faduwar gwamnatin Muammar Gadaffi of Libya, an samu bazuwar makamai daga kasar abin da kuma ya kara hassada rikice rikicen da ake fuskanta a sassan Najeriya a halin yanzu.

Buhari ya kuma kara da cewa, a kan matsalar jahar Zamfara, an dauki matakai da dama da suka hada da canza kusan dukkan jami’an ‘yan sanda da suka kai fiye da shekara uku suna aiki a jahar don tsaftace harkar tsaro da samar da zaman lafiya a jahar da ma kasat ta Najeriya baki daya.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More