Rufe iyakokin Najeriya baya nufin mungunta-Ministar Kudi

Ministar kudi da tsaretsare Zainab Ahmed Shamsuna, ta bayyana  cewar, Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna amincewa da rufe iyakokin Najeriya da makwabtanta saboda ya na sane da matsanancin halin da tattalin arzikin kasashen zai shiga. inda ta kara da cewa, tunda farko bai amince da matakin ba, don haka ba da mugun nufi a karshe ya amince da hakan ba. Zainab Ahmad ta sanar da hakan a ranar Lahadin da ta wuce a yayin da ta ke ganawa da manema labarai a babban birnin Washington DC da ke kasar Amurka, inda ministar ta ce an dauki matakin ne don gyara alakar Najeriya da makwabtanta.

A cewar Hajiya Zainab, bankin bayar da lamuni na duniya wato IMF na goyon bayan mataki, saboda tana da masaniyar cewa matakin ba ya nufin kuntata wa kasashen, sai dan yin gyara ga tsarin alakar kasuwanci a tsakanin kasashen.

An yi ta kokarin daidaitawa da sauran kasashen, amma hakan ya faskara. “Mun san akwai matsi ga tattalin arzikin kasashensu, dalilin daukar mataki, amma abinda mu ke so kasashen su gane shine, za su iya turo ma na kayayyaki, amma fa sai ta tashoshin jiragen ruwanmu,” in ji ta.

Inda ta  jaddada cewa, dole ne kayan su shigo Najeriya cikin tsari dan  baiwa hukumar kwastan ta qasar damar bincikar su, sannan kuma su dinga biyan duk wani harajin da ya kamata.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More