Ruga: Wasu gwamnonin Najeriya sun kalubalacin shirin

Shirin gwamnatin tarayyar Najeriya na samar da filayen kiwo ga Fulani na ci gaba da haifar da cece-kuce a kasarnan,yayin  da gwamnonin jahohin yankin kudu maso kudu da na kudu maso yamma suka yi fatali da shirin na Ruga, wajen  bayyana shirin a matsayin wani yunkuri ne na taimaka wa wata kabila da kudaden talakawa.

Mafi yawancin  wayanda  suka amince da wannan shiri na gwamnatin tarayya gwamnonin yankin arewa maso yamma da arewa maso gabashi da kuma wadansu gwamnoni daga arewa ta tsakiya.

Sai dai gwamnatin tarayya sun dage akan cewa shirin samar da Rugar Fulani a Najeriya zai magance rikicin manoma da makiyaya a kasar, sannan ba za su tilasta wa kowanne gwamna yin ammanna da  shirin ba.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More