Rundunar sojin saman Najeriya ta lalata sansanin ‘yan Boko Haram a Zamfara’

A karon farko rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da samuwar sansanin mayakan Boko Haram bangaren al-Barnawi wacce ake kira ISWAP.

Hakan ya biyo bayan wani samame da ta kai a wata mabuyarsu da ke Zamfara, rundunar ta ce ta kashe mayakan kungiyar da dama.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Najeriyan ta ce sakamakon wasu bayanan sirri da ta samu wadanda suka tabbatar da samuwar wadannan mayaka ya sanya ta kai wannan hari ta sama a ranar 10 ga watan Yuli.

BBC ta rawaito cewa,dakarun rundunar Operation Hadarin Daji ne suka kai simamen cikin dajin Kuyambana da ke kudu maso yammacin jahar ta Zamfara, a cewar sanarwar.

Sanarwar ta kara da cewa bayan tarwatsa sansanin wasu da dama daga cikin mayakan sun nemi tserewa a kan ababan hawa, wadanda suma aka bisu aka kashe su daga baya.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana takamaimai mutane nawa aka kashe ba ko kuma nawa aka kama ba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More