Sabanin kungiyar ASSU da gwamanatin tarayya:  Abunda minista Ngige ya fada

Ministan kwadago da samar da ayyukan Najeriya, Dr. Chris Ngige, ya yi magana game da sabanin da gwamnatin tarayya ta samu da kungiyar ASUU ta malaman Jami’o’i.

Bayan kamala taron majalisar zartarwa ta tarayya

da aka gudanar a fadar shugaban kasa na ranar Laraba ne  dakta Chris Ngige ya bayyana cewa haramtaccen yajin aiki kungiyar ASUU ta ke yi a dalilin tursasawa ‘Ya ‘yanta shiga cikin tsarin albashin na IPPIS da aka kawo.

Wannan shine karon farko da gwamnati ta yi magana game da yajin aikin kungiyar, da ya ke amsa tamboyoyin ‘Yan jarida, Ngige ya ce kungiyar ASUU ba ta sanar da gwamnatin tarayya halin da ta ke ciki ba, sai kurum ta tafi yajin aikin makonnni biyu.

Yana daga cikin rashin gaskiya ce a an biya wayanda sukayi yajin aikin albashi, don basu yi aiki ba  da suka kauracewa ofisoshin nasu, ya zama busa da hakki a kudin. Inji ministan kwadagon.

Inda ya kara da cewa, ma’aikatarsa ta shirya zama da kungiyar  ASUU a ranar Alhamis domin shawo kan sabanin da ya shiga tsakaninsu da gwamnatin, kuma kungiyar  ASUU za ta zauna da shi da ministan ilmi, ministar kudi da tattali da kuma babban akawutan Najeriya domin samun mafita.

Ko da Ministan ya na sa ran cewa gwamnatin Najeriya za ta shawo kan wannan yajin aiki, sai dai ya ce babu ma’aikacin da ya isa ya fadawa gwamnati yadda za a biyasa albashi, duba da cewa  yajin aikin da ASUU ta shiga bai halatta ba.

Gwamnatin dai ta dakatar da biyan albashin wadanda su ka guji IPPIS ne saboda rage fachakar kudi.

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More