Sai munga abunda ya ture wa Buzu nadi kan yan matan Chibok

Kungiyar BringBackOurGirls da ke fafutukar ganin an ceto ‘yan matan Chibok da Boko Haram ta sace, ta ce za ta ci gaba da matsin lamba ga gwamnati har sai an ceto sauran ‘yan matan.

Kungiyar ta jagoranci zaman tunawa da cika shekaru biyar da sace ‘yan matan 276 daga makarantarsu da ke garin Chibok a jahar Borno.

An yi nasarar kubutar da wasu daga cikinsu, amma akwai sauran ‘yan mata 112, wadanda har yanzu ba a san inda suke ba.

A wata sanarwa, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ba zai huta ba har sai ya sake hada ‘yan matan da iyayensu.

Emman Shehu Usman daya daga cikin jagororin kungiyar BBOG ya shaidawa BBC cewa abin kunya ne ga kasa kamar Najeriya ace a bar ‘yan mata a hannun ‘yan ta’adda har tsawon shekaru biyar ba tare an kubutar da su ba.

Kimanin  shekaru biyar Kenan da sace ‘yan matan, kuma an gudanar da gangami a biranen Abuja da London da Washington.

A wajen gangamin masu fafutukar da iyayen yaran sun jadadda bukatar kara kaimi wajen kubutar da sauran ‘yan mata 112 da suka rage hannun mayakan kungiyar Boko Haram wadanda suka sace su.

Mista Emman ya ce za su ci gaba da fafutika har sai an dawo da ‘yan sauran ‘yan matan da suka rage.

Zuwa yanzu babu wani tabbaci na cewa  yan matan da suka rage a hannun Boko Haram suna raye ko wani bayani kan inda ake garkuwa da su.

Wasu rahotanni sun ce an ga wadunsu a kasar Kamaru, sai dai  babu wata majiyar gwamnati da ta tabbatar da hakan.

Amma akwai wasu alamomin da suka nuna cewa yawancinsu sun yi aure har da ‘ya’ya.

An sace dalibai ‘yan matan ne ranar 14 ga watan Afrilun 2014, lamarin da ya dimauta al’ummar duniya, tare da janyo gangami da kiraye-kirayen lallai a ceto su.

 

 

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More