Sakataren gwamnatin jahar Ondo Abegunde ya yi murabu daga mukaminsa

Rahotunnin sun nuna cewa,  sakataren gwamnatin jahar Ondo, Mista Idefayo Abegunde, ya yi murabus daga mukaminsa a yau Litinin 6 ga watan Yuli 2020.

Abegunde,  ya mika takardar  barin aikin a safiyar yau Litinin, sai dai bai bayyana dalilan sa na barin aikin ba, inda yace cikin sa’o’i 24   zai bayyana inda ya sa gaba.

Gwamnan jahar Rotimi Akeredolu ne ya nada Abegunde a matsayin sakataren gwamnatin bayan kafuwar gwamnatin tasa a 2017.
 
Tsohon sakateran gwamnatin ya godewa gwamna Akeredolu kan damar da ya bashi na yi wa jahar sa hidima.
Sannan kuma yayi wa gwamnan fatan samun sauke, kasancewar sa a killace sakamakon  kamu da cutar Coronavirus da yayi.

Ina za ran hukumar zabe  mai zaman ta kasa wato INEC za ta gudanar da zaben kujerar gwamnan jahar  ta Ondo,   a  ranar  Asabar 10 ga watan  Oktoba.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More