Sakon shugba Buhari kan Maulidi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce, babban abin da musulmi za su yi domin tunawa da ranar haihuwar annabi Muhammad SAW shi ne su habbaka koyarwarsa a rayuwarsu da kuma  zamantakewarsu.

Buhari ya wallafa sakon mauludin ne a shafinsa na Twitter ranar Litinin, inda ya ce satar jama’a domin neman kudin fansa da kisan jama’a da yi wa mata auren dole duk sun saba da koyarwar addinin musulunci.

Shugaba Buhari ya ce ina yi wa daukacin musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Muhammadu SAW.

Babbar girmamawa da musulmi za su yi wa annabi ita ce habbaka halayensa na rashin son tayar da zaune tsaye da son zaman lafiya da kuma yin hakuri.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More