Sallar Layya: Ganduje yasa an fitar da fursunoni 29 a Kano

Gwamnan jahar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya saki fursunoni  guda 29 da ke zaman gidan gyaran hali na Goron – Dutsen a Kano.

Gwamnan da ya bayar da umurnin sakin fursunonin a yayin da ya kai ziyara gidan gyaran halin a ranar Juma’a  31 ga watan Yuli 2020, ya ce ya aikata hakan ne saboda bikin  Sallar Layya

Ganduje ya ce an yi la’akari da irin laifukan da suka aikata da kuma alamun sauyin halayensu yayin zaman su a gidan gyaran halin.

Inda ya kara da cewa dalilin ziyarar shine don nuna wa fursunonin cewa gwamnati ta san da zamansu kuma suma mazauna jahar Kano ne.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More