Sambo Dasuki na nan a raye – DSS

96

Normal
0

false
false
false

EN-US
X-NONE
X-NONE

/* Style Definitions */
table.MsoNormalTable
{mso-style-name:”Table Normal”;
mso-tstyle-rowband-size:0;
mso-tstyle-colband-size:0;
mso-style-noshow:yes;
mso-style-priority:99;
mso-style-parent:””;
mso-padding-alt:0cm 5.4pt 0cm 5.4pt;
mso-para-margin:0cm;
mso-para-margin-bottom:.0001pt;
mso-pagination:widow-orphan;
font-size:12.0pt;
font-family:Calibri;
mso-ascii-font-family:Calibri;
mso-ascii-theme-font:minor-latin;
mso-hansi-font-family:Calibri;
mso-hansi-theme-font:minor-latin;}

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta karyata labarin da ake ta yadawa na cewa tsohon mai bawa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro Kanal Sambo Dasuki ya rasu.

Kakakin hukumar Peter Afunanya ya shaida wa kafar talabijin ta kasa NTAcewa labarin karya ne ake yadawa, inda yace, “bai mutu ba ,kuma yana nan cikin  koshin lafiya.”

Ya kuma yi Allah wadai da labarin wanda ake ta yadawa a intanet, tare da yin kira ga jama’a su yi watsi da shi.

Sambo Dasuki ya shafe fiye da shekaru uku a tsare,tun watan Disamban 2015 hukumar DSS ke tsare da shi kan zargin wawushe kudin da aka ware domin sayo makaman yaki da Boko Haram.

Ana ci gaba da tsare Dasuki ne duk cewa da kotun tarayya ta sha ba da belin shi, har da kotun ECOWAS.

Gwamnatin Buhari dai ta dade tana cewa tana ci gaba da rike shi ne saboda ta daukaka kara.

‘Yan jaridar da suka ziyarci inda ake tsare da shi sun ce sun yi tozali da shi, inda suka jima suna hira har ya amince aka dauki hotonsa domin karyata labarin ya mutu.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More