Sani Garba SK na nan da ransa

Labarin  Fitaccen tauraron fina-finan  hausa wato Kannywood Sani Garba SK. na  Allah ya yi masa rasuwa ba gaskiya bane.

Wasu mutane sunyi  amfani da shafukan sada zumunta wajen yada  labaran karya na  cewa ya rasu bayan ya yi fama da doguwar rashin lafiya.

Duba da cewa dama tauraron na fama da rashin lafiya.

Sai dai OakTV Hausa ta zanta da mai bada umarnin shirye-shiryen fina-finan hausa  Darakta Hassan Giggs inda ya  tabbatar mana da cewa   jarumin Sani SK yana nan da ransa yana  karbar magani a asibitin  Nasarawa dake Jahar Kano, kuma yana samun sauki.

Giggs  ya kara da cewa Sani Garba SK yana famane da ciwon siga, amma tunda yanzu an gano hakan kuma yana karbar magana hakan na ba basu tabbacin cewa da yardar Allah zai samu sauki.

Haka a baya aka yada  labaran karya a kan mutuwar wasu fitattun taurarin Kannywood, ciki har da Sadiya Gyale da Sani Moda wani har yanzu sunan nan da ransu.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More