Sarakuna 3 ne kadai ba su da hannu a matsalar tsaron Zamfara

Kwamitin da gwamnan jahar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya kafa domin binciko abin da ke haddasa kashe-kashen da jahar ta tsinci kanta ciki ta mika rahotanta ga gwamnatin.

Kwamitin a karkasahin jagorancin tsohon Sufeto Janar na yan sandan Najeriya Muhammad D. Abubakar, ya bukaci a kori sarakuna biyar da uwayen kasa 33 da kuma hakimai da dama.

Sai dai wata majiya da ta bukaci a sakaya sunanta ta shaida wa Aminiya cewa sarakunan da ake zargi da hannun a sha’anin kashe-kashe da satar shanu a jahar sun wuce abin da kwamitin binciken ya nuna nesa ba kusa ba.

Su kwamitin binciken sun ce a sauke sarakuna biyar, to amma  a cikin sarakuna 17 na wannan jaha ta Zamfara, sarakuna uku ne kadai bincike ya tabbatar da ba su da wata alaka da wannan lamari, inji shi.

T

Shugaban Kwamitin Muhammad Abubakar,ya ce kwamitin nasa ya mika bukatar warware rawunan sarakunan ne bayan da ya same su da hannu dumu-dumu cikin lamuran rashin tsaron da ya addabi jahar shekara da shekaru,inda kwamitin ta ce wadansu daga cikin tubabbun yan bindigar da suka gana da su a lokacin zaman da suka yi da masu ruwa-da-tsaki, sune suka shaida musu cewa wadansu sarakunan na da hannu wurin tilasta musu daukar makamai.

Kwamitin ta bukaci gwamnati ta yi wa tsarin masarautun jahar garambawul, yana mai cewa sarakunan jahar sun zama tamkar maroka a hannun al’ummomin da suke mulki a jahar.

 

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More