Sarki Salma na kasar Saudiyya yana kwance a gadon asibiti

An kwantar da sarki Salman Bn Abdul’aziz na Saudiyya a wani asibitin Riyadh inda ake yi masa gwaje gwaje

Bayanai sun ce Sarkin mai shekara 84 na fama ne da rashin lafiyar da ta shafi mafitsara.

Da safiyar yau Litinin 20 ga watan Yuli ne Kamfanin dillacin labaran Saudiya SPA ya ruwaito cewa an kwantar da Sarki Salman asibitin na Riyadh ba tare da wani cikakken bayani ba.

Tun 2015 Sarkin ke mulki a Saudiyya – kafin zamansa Sarki ya shafe shekara kusan biyu a matsayin Yarima mai jiran gado kuma ya taba rike mukamin mataimakin firimiya a 2012.

Ya kuma shafe sama da shekaru 50 a matsayin gwamnan Riyadh.

BBC ta rawaito cewa, labarin rashin lafiyar Sarki Salman Yanzu ya sa hankali ya karkata ga makomar Saudiyya musamman zamanin Muhammad Bin Salman, Yarima mai jiran gado wanda tuni ake ganin shi ke tafiyar da jagorancin Saudiyya.

Yariman mai jiran gado shi ya kaddamar da sabbin sauye sauye na tattalin arziki na kokarin karkatar da dogaro da kasar Saudiyya ke yi da arzikin feitr.

Wannan ya sa Yariman mai shekara 34 ya samu karbuwa da goyon baya musamman tsakanin matasan Saudiyya na kawo wasu sabbin abubuwan da ba a taba gani ba a kasar musamman ba mata ‘yanci.

Amma wasu na bayyana damuwa kan nuna karfi iko akan kafofin watsa labarai da kuma kama karya da aka gani.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More